Dangane da zabe mai zuwa , wakiliyar sashin Hausa ta yi hira da wasu almajirai a yayin da wasu daga cikin su ke yinkurin sayar da katin zaben su, koda yake daya daga cikin su ya wayar masu da kai musamman agame da muhimmancin katin da kuma hatsarin sayar da shi.
Isah wani almajiri ne kuma shine wanda ya tsaya tsyin daka don ganin cewa abokan nasa basu sayar da katin zaben su ba saboda kuma su tabbatar sun yi anfani da shi domin wata dama ce muhimmiya suka samu.
A cewar sa “mu arba’in ne, amma nayi kokarin shawo kan abokai na kuma sun yarda baza su sayar da katunan ba kuma sun ce zasu kada kuri’a domin kwato ‘yancin kansu daga hannun shugabanin su”.
Daga karshe yace uku daga cikin arba’in dinne kadai suka ce lallai zasu sayar da katunan su zasu yi da zarar mai saye ya samu, ya kuma yi kira ga daukacin matasa da su kasance masu hankali da kuma yin anfani da kuri'ar su domin samar ma kansu da kuma kasar su abin da ya kamata.