Wasu 'Yan Gudun Hijira Sun Sami Taimako

FILE

Bikin ranar mata ta duniya mai suna mugani a kasa dai wato (make it happenda) da turanci a jahar kano , wata kungiyar al’uma mai suna citizen united for peace and security ce ta gudanar da wani bada tallafin kaya ga ‘yan gudun hijira 200 da matsalar boko haram ta raba da gidajen su daga jahohin Yobe , Adamawa, Borno da kuma wasu daga central Africa wato Bangi.

Bayan wa’azi da bayanan kiwon lafiya da aka basu, Dr Fatima it ace mace kadai da ta samo kudi daga ‘yan uwa da abokan arziki ta hanyoyin sadarwa kamar su faceboo da watsap ta kuma kaddamar da wannan tallafi ta hanyar wannnan kungiyar wato citizens united for peace and security.

A cewar ta “duk da gwamnati na taimakaw mutanen nan muma ya kamata mu taimaka sai kawai na fara tuntubar jama’a kuma duk wandanda nayi Magana da su babu wanda yace a’a, haka muka tara wadannan kudai kuma naga ya dace inbi ta hanyar wannna kungiyar tunda muna tare da su a kowane lokaci”.

Daga karshe jama’ar da suka karu da wannan tallafi sun yi matukar gadiya da nuna farin cikn su musamman ta yadda suke cikin wani hali na neman taimako kuma gwargwadon hali kowannen su da ke a wannan wurin ya sami tallafin.