Ya Ake Gane Rena Kyauta Daga Masoya

Kamar yadda muka saba jin ra’ayoyin matasa maza da mata akan batutuwan da suka shafi al’amuran samartaka, soyayya, zaman aure da abubuwa masu alaka da zamantakewa da halayyar dan’adam, maudu’in mu na wannan makon shine, “Rena kyauta”.

Jama’a da dama sun bayyana yadda abokan soyayya ke faranta masu zuciya musamman ta hanyar bada kyauta komai kankantar ta. Haka kuma wasu kan yi amfani da hannun baiwa domin jan ra’ayin abokan soyayya cikin sauki, musamman ganin yadda ake alakanta mutuum mai yawan bada kyauta da kyakkywar zuciya.

Ku Duba Wannan Ma Ramson-G: Sana'ar Waka Ba Ta Mutanen Banza Bane

Kodashike wasu kan yi amfani da irin wannan dabara ta bada kayuta domin yaudara, masu iya Magana sun ce, “idan bera dda sata, to daddawa ma nada wari” dalili kuwa shine kwadayin abin duniya kan jefa matasa da dama cikin halin da na sani.

Matasa da dama sun bayyana cewa basa rena kyauta komai kankantarta musamman daga masoyi ko masoyiya, duk da cewa ba a taru an zama daya ba, amma yawanci basa mayar da hankali wajan fahimtar ko kyautar da suka bada ta sami karbuwa dari bias dari kokuma wanda suka ba kyautar ya Allah mace ko namiji ya rena.

Ka/kin taba bada kyauta aka rena? Kun taba tunanin tsayawa ku lura ko kyautar da kuka ba masoyanku ta sami karbuwa dari bisa dari?, bayyana ra’ayi.