Yaya Toure Zai Bar Kulab Din Manchester City

Dan bugun tamaular nan Yaya Toure ya fada cikin kungiyar kwallon kafa ta Inter-Milan bayan mataimakin shugabanta Javier Zanetti yace an samu matsaya maganar kwantiragi.

Dan wasan tsakiyar filin dan kasar Ivory Coast zai bar Manchester City a karshen kakar wasan nan, sannan akwai yiwuwar ya sake hadewa da tsohon Maigidansa Roberto Mancini a kasar Italiya.

Toure dai shine mafi tsada a kulub dinsa na City, domin yana kwasar albashin kusan Fam na Ingila Dubu 200 da 20 a duk mako, sannan ya sa hannu a kwangilar Shekaru 4 ne da su a watan Afrilun shekarar 2013.