Zaman Gidan Yari Akan Kwalbar Manja

Wata kotu a jihar Nasarawa ta yankewa wani matashi Sunday Anthony, mai zama a Jankawa Masaka, na jihar hukunci zaman watani tara a gidan yari bisa laifin satar kwalbar manja.

Mai shara’a Yakubu Ishaku, wanda ya zartar da hukuncin bayan da mai laifin ya amsa laifinsa kuma ya nemi kotu ta yi masa afuwa sai kotu ta bashi zabin biyan tarar Naira dubu goma.

Tunda farko mai gabatar da kara Frank Swem, ya fadawa kotu cewa ranar 2, ga watan Janairu 2018, da misalign kafe shida na yamma Sunday Anthony, ya shiga dakin makwabcinsa inda yayi awon gaba da kwalbar manja da mudun wake sittin da biyu da kudinsu ya kai kusan Naira dubu talatin.

Ya kara da cewa wannan ya sabawa sashe na 348 da 287 na dokokin shara’a wanda aka fi sani da Penal Code.