Zanga Zangar Matasa A Filin Jiragen Saman Mallam Aminu Kano

Jirgin saman Malam Aminu Kano.

Gamayyar kungiyoyin matasan arewa sunyi zanga zanga a filin jirgin sama na malam Aminu dake Kano suna neman karin bayani daga hukumimin Najeriya dangane da jirgin dakon kaya na Rasha makare da makamai da jami'an tsaro suka kama a filin jirgin na Kano a shekaran jiya Asabar.

Wakilinmu na Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya halarci wurin zanga zangar kuma ya zanta da shugaban zanga zangar Ibrahim Garba Wala, inda shugaban ya fadi dalilin su na fitowa domin su nuna damuwar kan jirgin da aka gayawa duniya yayi saukar bazata a filin jiragen sama na mallam Aminu Kano, wanda acikin jirgin aka samu jirage masu saukar ungulu biyu, da wata motar Jeep kirar Ford harma da akwatuna dauke da dinbin makamai.

Kuma ya kara da cewa wannan ba karo na farko bane da ake jin cewar an kama ko an sami makamai ta filin jirgin mallam Aminu Kano, dalili kuma shine a cikin wannan tsanani na masifa da ake ciki na kashe kashe ake yiwa ‘yan Arewa, muntabbata cewa al’ummar Najeriya na son jin ta inda maharan ke samun ire iren muggan makaman da suke amfani dasu inji Ibrahim Garba Wala.

Sude gamayyar kungiyoyin matasan dai na son hukumar Najeriya ta fito tayi musu bayani a matsayinsu na ‘yan kasa kuma wakilai na al’ummar Najeriya cewa, wannan kayan nawanene kuma ina ya dosa.

Jami’an tsaro dai sun fadawa matasan dasu jira za’ayi musu bayani, kasancewar Jami’an na cikin wani taro.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaban Matasa Ibrahim Garba Wala - 2'33"