Zauran Matasa – Kan Shaye Shaye Da Neman Mata

Drug

A cikin zauran matasa da wakiliyar mu Madina Dauda ta jagoranta, an tattauna ne kan ire-iren cututtuka dake damun matasa a Najeriya dama nahiyar Afirka baki ‘daya.

Kadan daga cikini cututtukan dake damun matasa musammam a Najeriya, sune amfani da miyagun kwayoyi, rashin ilimin jima’i inji Mohammed Girema Bukakar, wanda yace miyagun kwayoyi na ‘daya daga cikin cututtukan dake yiwa matasa maza da mata illa, kasancewar yawan matasan dake shan kwayoyi na da yawa a wannan zamani.

Kwanakin baya ne akayi wani nazari inda aka gano cewa yawan matan dake amfani da kwayar Carden wanda a hausa ake kira (kodin), mafi yawancin su sun fito daga birnin Kano, matan kuwa dake amfani da kwayar shekarunsu ya fara daga 18 zuwa 35. Matasan dai na shan ire-iren wannan kwayoyi batare da iznin likita ba, kuma yawan kwayar da suke amfani da ita ta wuce haddin da likitoci ke bada izinin sha. Hakan na kawowa yawan matasan dake shan kwayoyin tabuwar hankali, kwashi casa’in da biyar na mahaukata idan aka duba kwayoyi ne yakai su halin da suke ciki.

Rashin wadataccen ilimin jima’i na ‘daya daga cikin cututtukan dake damun matasa, rashin yin amfani da ilimin jima’i da addini ya koyar ya jefa matasa cikin halin ‘daukar wasu cututtuka da suka hada da cuta mai karya garkuwar jiki. Kalubale game da wannan cuta kuwa shine matasa da dama na tsoro da fargabar zuwa a duba su a asibiti, domin a basu kulawar data kamata da ilimantar dasu kan cutar, amma rashin yin hakan shike janyo yada cutar ga mutanen da basu ji ba, basu gani ba.