A tattaunawar da wakilin mu Muhmud Ibrahim Kwari yayi da wasu matasa masu sayarwa da gyaran kan wayar salula a kano, sun tattauna ne kan yadda suke gudanar da sana’ar su da kuma hanyoyin da suke ilimantar da kansu a duk lokacin da sabuwar waya ta fito.
Matasan dai sun bayyana yadda suke amfani da na’urar kwamfuta wajen sana’ar su ta gyaran wayoyin hannu, kasancewar rashin zuwa makaranta don koyon wannan sana’a tasu, suna amfani da shafin yanar gizo domin bincike da kara wa kansu ilimi domin bunkasa sana’ar su.
Akan yanar gizo akwai wasu dandali masu yawa da mutane ke haduwa domin tattaunawa da kara wa juna ilmi a fannoni daban daban, haka suma masu gyaran wayoyin hannu suna da irin wannan dandali inda suke haduwa da tattaunawa akan sana’ar su, da ilimantar da juna kan sababbin wayoyin hannu da suke fitowa a wannan zamani.
Mafi yawancin mutanen dake wannan sana’a ta sayar da waya dakuma gyaran waya matasa ne, hakan na faruwa ne kasancewar wannan sana’a tafi dacewa da su matasan, idan aka duba wajen yin amfani da kayan zamani kamar yanar gizo wajen binciken ire iren na’urorin, haka zalika sababbin fasahohi na fitowa a kullun.
Fitowar wayoyin hannu a wannan zamani sun taimaka kwarai da gaske wajen samarwa da matasa aikin yi, matasa ‘yan shekaru goma sha takwas zuwa kasa da arba’in ne ke wannan aiki, kuma anyi kiyasin matasa kimanin dubu hamsin ne a jihar Kano suka sami aikin yi a fannin sayarwa da gyaran wayar hannu.