ZAUREN MATASA: Yaya Kuke Ganin Kamun Ludayin Wannan Sabuwar Gwamnati

A zauren matasa na shirin yau da gobe shirin matasa, Madina Dauda ta sami zanatawa da wasu matasa da dama inda suka tofa albarkacin bakin su akan yadda suka ga kamun ludayin wannan sabuwar zababbiyar gwamnati a karkashin mulkin Muhammadu Buhari.

Zauren ya fara jin tabakin matashi mai suna Muhammad Bukar Girema, wanda ya bayyana cewa “idan aka duba yadda dalilan da suka sa mutane suka zabi shugaba Muhammadu Buhari sun kasu kashi uku, na farko akwai tsaro, na biyu kuma akwai magance cin hanci da rashawa, da kuma samar da ayyukan yi. Dan haka duk wanda ya duba zai ga cewa harkokin tsaro sun inganta a yankin arewa maso gabashin Najeriya, kuma kowane dan arewa yasan cewar zai iya sa suturar da yaga dama ya shiga inda yaga dam aba tare da fargaba ba.

A fanninn yaki da cin hanci da rashawa kuma shugaban kasa na cigaba da yin iya bakin kokarin sa domin ganin cewa an kwato duk kudaden da wasu ‘yan kasa suka sace musamman kudaden da aka fitar domin sayen makamai a yaki kungiyar boko haram.”

Da zauren ya waiwaya domin tabakin malama Hafsat Zaki, matashiyar ta bayyana cewa “daya daga cikin abin da ta gani a kasa shine zaman lafiya da kwanciyar hankali, amma gaskiya ta banagren abinci mutane na wahala, domin yunwa ba karamar cuta bace musamman duba da yadda matasa da dama suka fara sata ko kwacen kayan jama’a duk saboda yanayin kuncin halin tayuwa da suka sami kansu, dan haka gwamnati ta taimaka ta duba wannan yanayi da ake ciki”.

Ta kara da cewa a cikin abubuwa uku da mai Magana na farko ya furta, kawo yanzu abu guda kadai suka samu wato tsaro, amma a cewar ta matasa na cikin mawuyacin hali domin da dama cikin wadanda ke da ayyukan yi ma sun rasa saboda wasu dalilai.

Ga cikakkiyar hirar.