Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Dokar Hana Fita Waje Dare Da Rana A Ibbin Jihar Taraba - 5/4/2014


An kafa dokar hana fita dare da rana a garin Ibi na Jihar Taraba, a wani yunkurin murkushe yiwuwar tashin hankali a tsakanin kabilu dabam-dabam dake wannan gari.

Wannan lamarin ya faru ne a bayan da wasu mutanen da ba a san ko su wanene ba suka kashe wasu Hausawa masunta su biyu, suka raunata na ukunsu. A lokacin da labari ya bazu a gari cewa wasu 'yan kabilar Jukun ne suka kashe su, sai aka so a samu tashin hankali, inda wasu matasan Hausawa suka yi barazanar daukar fansa.

Wannan shi yasa nan take hukuma ta kafa dokar hana fita waje baki daya, inda aka zuba jami'an tsaro a kan tituna domin hana yiwuwar daukar fansar.

Wannan lamarin yana zuwa ne kasa da kwana guda a bayan da shugabannin Jukun, Fulani da Tiv suka rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya a Jihar Taraba.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00
Direct link
XS
SM
MD
LG