WASHINGTON, DC —
A hirar da yayi da VOA Hausa,w ani sojan Najeriya dake bakin daga a Jihar Borno, yace su a ganinsu sojojin da suka je can da zummar kawo karshen tashin hankali, za a iya murkushe Boko Haram cikin kwana guda idan ana da niyyar hakan, amma da alamun manyan sojoji su na amfani da su kananan ne kawai don ci gaba da samun kudi.
Yace an taba gayyatar bataliyarsu a kan tazo ta rufa ma wata bataliyar da zata shiga daji baya, amma da suka je sai kwamandan wancan bataliyar ya raba musu riguna kala dabam-dabam, kuma da aka je bakin dagar, sai ya janye sojojinsa da tankokinsu, aka barsu da bindigoginsu kawai su na fuskantar mayaka dauke da manyan makamai na harbo jiragen sama masu iya harbin mutum daga can nesa.
Haka kuma, yayi zargin cewa a lokacin artabun, sun ga wasu sojojin da suka koyar da su yadda ake yaki da ta'addanci a Kontagora su na yaki tare da 'yan Boko Haram din. Ma'ana dai, kamar da wata kullalliyar a wannan lamarin.
Sojan yayi zargin cewa ba a biyansu hakkokinsu, domin yayi watanni fiye da 3 a cikin daji, amma ko Naira dubu 50 bai samu ba.
Ga dai kashin farko na wannan hira mai tsawon minti 4