WASHINGTON, DC —
Wata kotu a cibiyar hada hadar kudi ta Indiya ta yanke hukumcin kisa kan wasu mazaje uku a saboda hannu a wasu ayyukan fyade guda 2.
Wannan shi ne karon farko da aka yanke hukumcin kisa a kan wadanda suka yi fyaden da bai haddasa mutuwar wadda aka yi ma ba tun lokacin da Indiya ta kara tsananta hukumcvin fyade.
Mutanen uku da aka yanke ma hukumcin kisa yau jumma’a a birnin Mumbai, an same su da laifin taruwa da yi ma wata ‘yar jarida mai daukar hoto fyade a watan Agustar 2013. Haka kuma an same su da laifin yi ma w3ata matar fyade wata guda kafin nan a cikin wata tsohuwar masakar da suka yi ma ‘yar jaridar fyade.
Haka kuma a yau Jumma’ar, wata kotu a kudancin Indiya ta soke sallamar wasu mazaje su 24 da aka yi dangane da batun wata budurwar da aka yi mata fyade na tsawon makonni shekaru 18 da suak shige.
Babbar kotun Kerala ta yanke hukumcin daurin rai da rai kan mutum guda, sauran 23 kuma aka yanke musu hukumcin daurin da ya kama daga shekaru 7 zuwa 11.