An cafke wani tsohon Malami makaranta, Onuzuluike Ude, wanda ake zargi da buga kudi na jabu dama takardar shedar gama karatu na makarantu daban daban, har ma da na kammala yiwa kasa hidima wato NYSC.
Ude, dan shekaru saba’in da biyar an kama shine a jihar Anambra, tare da wata mata Evelyn Nwoke, wace take taimaka masa gudanar da wannan aiki.
Evelyn, tace bata san cewa takardun na jabu bane, amma ta amsa cewa Ude, yakan kawo mata wasu tarkardu da take canja masa wasu abubuwa akai.
Da yake tabbatar da labarin Kwamishinan ‘yan Sanda, Mr. Hosea Karma, yace yayi mamaki tsohon Malamin Makaranta zai sa kansa a harkar takardun makaranta na jabu.
Kwamishinan, yace takardun shedar da aka samu a wurinsa sun hada da ta Jami’ar Najeriya Nsuka, Jami’ar Nnamdi Azikwe, da makarantar kimiya da fasaha ta Gwamnatin dake Oko da kuma kwalejin horas da Malamai na Umunze, ya kara da cewa da zaran an kammala bincike za’a gurfanar dasu a gaban kotu.