Duk kokarin da hukumomin kasar Nijar suke yi akan hana tafiye tafiye mutane masu son zuwa kasar waje ta Hamada, alamarin masu son zuwa kasar Algeria na ciwa hukumomin tuwo a kwarya.
Hukumomi a gundumdar Arlit ta jahar Agadas sun bayana maido da masu son tsallakawa kasan Turai ta Hamada, su kimanin dari tara da tamanin da daya wanda yanzu haka suna kokarin mayar da su kasashen su.
Yace akwai masu tahowa masamman domin tsallakawa amma batare da sanin anihin kasar da zasu ba yana, yana mai cewa yanzu an maida wannan harka fataucin da Adam.
Ya kara da cewa babban abin yi shine dai a ci gaba da wayarwa matasa kai da yin kiraye kiraye kan irin hatsarin dake tattare da wannan tafiya mai hatsarin gaske.
A cikin wannan satin kuma an tsinci wasu mutane takwas dajin Sahara wadanda ake zargin cewa kishin ruwa ne ya kashe su.