Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wadanne Abubuwa Samari Da 'Yan Mata Ya Kamata Su Yi La'akari Dasu Wajan zabar Abokan Aure


Shirin samartaka na wannan makon na wannan makon ya sami jin ra’ayoyin matasa maza da mata ne domin jin ra’ayoyin su dangane da irin abubuwan da suka kamata matasa maza da mata su yi la’akari da su wajan zabar wadanda za su aura.

Ywancin samarin sun nuna kokuma danganta lamarin da tarbiyyar gida, ko da shike yawancin lokuta a cewar wasu wannan bashi da wani tasiri domin kuwa bai zama dole yara su taso da tarbiyya irin ta iyayen suba.

Da muka waiwaya wajan ‘yan mata, yawancin su sun nuna cewar neman ra’ayoyin jama’a kusa da inda saurayi ke zama nada tasiri kwarai domin kuwa a cewar su, dole ne mai hali ya nuna halinsa dan haka za’a iya gano halin saurayi cikin sauki.

Masu iya Magana sun ce so hana ganin laifi, idan so yayi nisa akan take duk wani rashin can canta amma daga karshe abin ya zama dana sani.

Ga cikakken shirin.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG