WASHINGTON, DC —
Emmanuel Adebayor, ya tabbatar da cewa zai bar kulub dinsa Crystal Palace bayan kammala wasan zakarun Turai na karshe.
Dan wasan mai shekaru 23 a duniya, ya rattaba hannu kan yarjejeniya da kulub din a watan Janairu, amma ba kasafai yake ake saka shi cikin wasa ba, kwallo guda kacal ya jefawa kulub din.
Emmanuel yace tafiyar a Crystal Palace tazo karshe a wannan watan na Mayu, amma ba tana nufin karshen sa ba kenan, domin zai ci gaba zuwa duk inda Allah ya kaisahi.
Ya ci gaba da cewa, a koda yaushe yana mai yiwa kulub din fatan alkairi, yana kuma son Cristal Palace ya lashe kofin wasan zakarun Turai da zasu buga.