Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ofishin Jakadancin Faransa Ya Hana Wasu 'yan Wasan Super Eagles Takardar Izinin Shiga Kasar


Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta bayyana cewa ofishin jakadancin Faransa ya hana wasu daga cikin jami’anta da kuma ‘yan wasan kungiyar Super Eagles takardar izinin shiga kasar a yayin da suke shirin tafiya kasar domin gudanar da wasu wasanni a cikin wannan watan da muke ciki.

A cewar rahotanni daga hukumar, wasu ‘yan wasa da ke da zama a gida ne da kuma kwac kwac guda biyu, sai kuma wasu daga cikin jami’an hukumar ne ofishin jakadancin ya hana takardun izinin shiga kasar ta Faransa.

Babban sakataren hukumar Malam Mohammed Sanusi ya ce ya kamata ofishin jakadancin ya sake duba lamarin domin ba jami’an takardar shiga kasar, ya kara da cewa jami’an da kungiyar ‘yan wasan zasu je kasar ne domin gudanar da wasanni masu muhimmanci.

Rahotannin sun bayyana cewa a yau laraba kashi sittin a cikin dari %60 na fasfo fasfo din ‘yan wasan ne aka dawo da suba tare da an amince masu shiga kasar ta Faransa ba.

Ana sa ran kungiyar Super Eagles ta Najeriya zata kara da Mali, da kuma kasar Faransa a ranar 27 na wannan watan da muke ciki, da kuma 1 ga wata mai hawa.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG