Wasu matasa da ake zargin 'yan bangar siyasa ne sun sa wa gidan sanata Kabiru Gaya wuta a karamar hukumar Gaya dake jahar Kano.
Matasan sun kuma kona ofishin kamfe da kuma gidan kajin dan majalisar wakilai Alhaji Abdullahi Mohammed dake kusa duk a yanki guda. Shaidun gani da ido sun bayyana wa mujallar (NAN) cewar lamarin ya afku ne a yau laraba da misalin karfe 11am na safe.
Shaidun sun kara da cewa matasan sun fara zanga zanga ne da ikirarin cewa 'yan siyasar biyu basu cika masu alkawarin da suka dauka ba a lokcin da suke yakin neman zabe a shekarar 2015.
Rahotanni sun bayyana cewa da farko jami'an tsaro sun tarwatsa matasan wadanda daga baya suka sake haduwa sa'annan suka aikata wannan mugunyar aika aika, daga bisani ma sun yi yinkurin kona gidan ciyaman din karamar hukumar Gaya amma jami'an tsaro suka taka masu burki.