WASHINGTON, DC —
Dan wasan kungiyar Chelsea, John Terry, ya amince ci gaba da buwaga kungiyar wasa har na tsawon shekara daya.
A baya dai ana tunanin Terry zai bar kungiyar bayan da yarjejeniyarsa ta kawo karshe, inda ake zaton zai koma bugawa MLS wasa ko ya tafi China.
Sai gashi a makon da ya gabata Chelsea tayi masa tayin sabunta kwantiraginsa don bugawa kungiyar wasa. Shugaban kungiyar Bruce Buck, ya ce yana mai matukar farin ciki da ganin cewa Terry zai ci gaba da bugawa kungiyar wasa.
Buck, ya kara da cewa Terry ya jagoranci kungiyar Chelsea, cikin mawuyacin lokaci a tarihin kungiyar.