Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jawabi Ga Masu Shirin Aure Daga Baba Musa


Kamar yadda muka saba a kowa ne karshen mako, mukan gayyaci iyaye ko kwararru domin samun shawarwari masu amfani da kuma bayanai musamman wadanda zasu taimakawa matasa.

Dan haka ne a wannan karon muka sami bakuncin dattijo kuma uba malam Baba Musa wanda yayi mana bayani akan irin abubuwan da yakamata matasa masu niyyar aure su yi la'akari da su a yayin da suke shirye shiryen zaben abokan zama.

Da farko ya bayyana cewa sanin asali na daya daga cikin manyan abubuwan da ya kamata a yi la'akari da su domin kuwa a cewar sa baya ga umurnin addini, duk wani abu da zai biyo baya bai wuce asali nagari ba.

Malamin ya kara da cewa yawancin matasa kan sami matsala wajan zaben matan da zasu aura domin son zuciya, wato idon su kan rufe domin wasu dalilan da basu da amfani daga karshe kuma su fara da na sani.

Ga cikkaken banin da yayi mana.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG