Kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASSU, ta bayyana cewa malan suna bin gwamnatin kasar bashin kudin alawus alawus har zunzurutun kudi Naira Biliyan 12, daga shekarar 2013, zuwa shekarar 2016, da kuma wasu Naira Biliyan 49, da suka sake taruwa daga ariyas din su.
‘Yayan kungiyar reshen Calabar a wani taron manema labarai sun bayyana cewa lamarin na ci gaba da shafar jami’o’in dake yankin, inda suka yi gargadin cewa babu tabbacin wata kariya ga makarantun jami’o’in a sakamakon rashin tabbacin dorewar al’amurra.
Jami’o’in dake yankin sun hada da jami’ar Calabar, da jami’ar Uyo, da Cross River da ta jihar Akwa Ibom, da jihar Abia da kuma Ebonyi.
Shugaban kungiyar Dr Tony Eyang, wanda ya yi jawabi a madadin sauran abokan aikin sa, a taron manema lkabarai a Calabar ya ce rashin magance tarin matsalolin da suka yi wa harkokin ilimi katutu na iya gurgunta harkokin ilimin Najeriya baki daya.