Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rawar Da 'Yan Najeriya Ke Takawa A Wasan Tamola Baya Misaltuwa A Duniya!


Dan wasan kwallon Najeriya, Brown Ideye
Dan wasan kwallon Najeriya, Brown Ideye

Tsohon mai tsaron gida na kungiyar kwallon kafar Super Eagle, Brown Ideye, ya saka ma sabon klob din shi kwallon ban-mamaki a karon farko, cikin wasan da suka buga farkon wannan satin.

Mai tsaron gidan dai ya taka rawa wajen ganin klob din shi, sun shiga gasar zakaru na “Greek Super League” da za'a gabatar nan da 'yan kwanaki, ‘yan wasan sunyi ma kungiyar Lacklustre Veria FC ci shida da daya.

Shigar dan wasan fili ke da wuya, sai ga kungiyar tasu ta fara kai farmaki, inda suka dinga zura kwallaye har shida. Shima dan wasa Paulo Bento, ya taka rawa wajen samun wannan nasarar, duk dai da cewar dan Najeriyar Brown, shi ne wanda ya share ma ‘yan klob din nasu fage.

Hakan na nuni da cewar matasa 'yan najeruya, kan iya taka rawar gani a wasan ta mola idan suka maida hankali yadda ya kamata.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG