Wani bincike da aka gudanar a kasar Birtaniya, ya bayyanar da kashi uku na masoya kwallon kafa na kallon wasannin Premier ta barauniyar hanya. A binkcike da aka gunara da matasa suka amsa yadda suke kallon kwallo, ya tabbatar da cewar mafi akasarin su, suna kallo ta hanyar satar kallo.
Mafi akasarin samarin, suna amfani da shafin Kodi Boxes, wajen kallon kwallo, wadanda shafufukan basu da lasisi na kallon wasannin, shafufuka irin su Sky, da BT, sune aka amincima su watsa wasannin kai tsaye.
Kasar dai nada kwararan hukunce-hukunce, idan aka samu mutun da kalo ta barauniyar hanya, ko kuma bama wasu damar kallo, za’a gurfanar da mutun a gaban kuliya.
A cewar Mr. Kieron Sharp, darekta a ma’aikatar shari’a, ya bayyanar da cewar wannan babban laifine, wanda idan aka samu mutun da aikawa zai fuskanci fushin hukuma. Babu wani dalili da zai sa mutun yace baisan wannan laifi bane.
Donmin an bayyanar da wannan aikin tun a wani zama da kotun koli ta kasashen turai tayi, duk wanda yake kallon kodai wasannin kwallo, ko finafinai da basu da rijistar sayarwa, ko kallon wadannan wasannin shima zai shiga cikin wani hali idan aka samu mutun da aikata laifin.
Facebook Forum