Masana kimiyya na gwamnatin Amurka, na amfani da hanyar sadarwa ta Twitter domin gano inda ake girgizar a fadin duniya.
Tun shekara ta 2009 masu nazari da kula da ma’adanan karkashin kasa, suka hada gwiwa da kamfanin Twitter, domin samin harsashe na gaskiya, da kuma ankarar da al’umma kafin aukuwar bala’in girgizar kasa.
Sai dai masana kimiyyar na dawwama ne ga al’umma wajen samun ire-iren wannan bayanai, idan har aka rubuta “Girgizar kasa” a shafin twitter to duk inda mutum yake a fadin duniya, kuma ko da wanne irin yare aka rubuta, to zai taimakawa masana kimiyyar Amurka, wajen nema da sanin abinda ke faruwa.
Masu Ilimin kimiyya na gwamnatin Amurka, sun biya kamfanin Twitter wasu kudade domin amfani da manhajar Twitter, wajen bibiyar wasu kalmomi na musamman a duk lokacin da wani cikin mutane miliyan 316 masu amfani da Twitter suka rubuta, kamar duk lokacin da wani yace ana girgizar kasa to alokacin masana kimiyyar zasu duba inda akeyi da ma inda ta nufa.
A cewar wani mai ilimin kimiyya kuma mai bincike yace, wannan hanyar na taimakawa sosai da sosai saboda wani lokaci na’urar da suka kakkafa a fadin duniya bata ganowa, wani lokaci kuma karfinta bai kai inda akeyi ba.
Girgizar kasa masu yawa da suka auku a yan shekarun da suka gabata sun taimkawa masana kimiyyar wajen gano muhimman bayanai, sun kuma koyi amfani da yaruka masu yawa wajen gano sahihancin abin da aka rubuta kan Twitter.