Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zargin Boko Haram Da Satar Wasu Italiyawa 2 Da 'Yar Canada Daya A Arewacin Kamaru - 5/4/2014


Wani Bafaranshe da 'yan Boko Haram suka taba sacewa a Kamaru suka sako shi daga baya.
Wani Bafaranshe da 'yan Boko Haram suka taba sacewa a Kamaru suka sako shi daga baya.
Jami’ai a kasar Italiya sun ce wasu ‘yan bindigar da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun sace wasu ma'aikatan coci biyu ‘yan kasar Italiya da wata mace mai aikin addini ‘yar kasar Canada a yankin arewacin kamaru.

Hukumomi sun ce an sace mutanen ne a cikin darenm jumma’a zuwa asubahin yau asabar a kusa da bakin iyakar kasar ta Kamaru da Najeriya.

Sace ‘yan kasashen yammaci ya zamo ruwan dare a wannan yankin bakin iyaka na Najeriya da Kamaru inda ba mutane da yawa, yake kuma da duwatsu da dazuzzuka.

An bayyana ma’aikatan addinin da aka sace din da cewa sune Giampaolo Marta da Gianantonio Allegri, dukkansu daga gundumar Vicenza a yankin arewa maso gabashin Italiya.

Ba a bayyana sunan macen ‘yar kasar Canada b.
XS
SM
MD
LG