Kamar yadda fasahar yada labarai ta bunkasa akan duniyar yanar gizo, akwai hanyoyin sadarwa masu yawa a wannan zamani da mutane ke amfani dasu wajen yada labarai, manufofi, harma da tallace tallace. Kan wannan batu ne muka gayyaci kwararran masanin fasaha Salisu Hassan na duniyar kwamfuta, wanda ya bamu haske kan shafin Blog.
Blog dai shafi ne akan yanar gizo da mutane ko kungiya ke amfani da shi domin saka rubutattun bayanai da hotuna wanda mutane zasuyi amfani da su wajen karantawa, ya kunshi labarai ko wasu manufofi. Duk mai sha’awa na iya mallakar wannan shafi na Blog domin yada manufofin sa.
Kamar shafin duniyar kwamfuta duniyarcomputer.com na daya daga cikin jerin shafukan Blog, domin mutum daya ne ya kirkireshi shi ya kuma mallake shi domin yada manufofinsa na wayar da kan al’ummar Hausawa kan fasahar kwamfuta, dama duk shafin da mutanen da basu wuce biyar ba suka bude ana iya kiran wannan shafi Blog.
Akwai hanyoyi da dama idan mutum yana son ya mallaki Blog, na farko za’a iya goya shafinka a bayan wata kungiya da suka bude shafi suka baiwa al’umma damar ikon kirkirar nasu shafin domin yada manufarsu, hanya ta biyu kuma mutum zai iya zuwa ya sayi suna da gurin da zai iya ajiye bayanan sa kan yanar gizo.