A cigaban tattaunawar wakilinmu Muhmud Ibrahim Kwari, da wasu matasa masu sana’ar sayar da wayoyin hannu a birnin kano, sunyi wannan muhawara ne akan harkokin sana’ar su da irin rawar da suke takawa domin bunkasa wannan sana’a.
Duk da yake matasan nada kungiya domin hada kan matasan da duk sauran masu sayar da wayar hannu a wannan kasuwa, Muhmud ya tambayi daya daga cikin matasan yadda matsayin hukuma ga masu wannan sana’a. inda Yunusa ya tabbatar da cewa kwarai da gaske hukuma ta shigo musammam ma lokacin da Mallam Ibrahim Shekarau, ke gwamna a jihar Kano, wanda har gwamnatin ta nema musu guri a palm center inda suke gudanar da wannan sana’a.
Kalubale da suke samu a yanzu haka shine tun lokacin gwamna Ibrahim Shekarau, basu samin wutar lantarki a gurin da suke kasuwancin su idan aka duba za’a ga wutar lantarki na da muhimmin amfani ga wannan sana’a, amma gwamnatin yanzu tayi yunkurin samar da wani shiri tare da kungiyar masu sana’ar waya da wata kungiya mai zaman kanta ta kimiyya da fasaha, inda za’a rinka baiwa mutane horo domin ganin an samar wa da matasa aikin yi.
Jihar kano na daya daga cikin manyan jihohi da ake hada-hadar waya a Najeriya, matasan na amfani da hanyoyi daban daban wajen samo kayan aikin su na gyaran wayoyi dama saro wayoyin da suke sayarwa tayin amfani da kasashen waje dama cikin gida.