WASHINGTON, D.C. —
Hukumar ‘Matasa ‘Yan Bautar Kasa a Najeriya, NYSC, na ankarar da matasa da ma sauran jama’a, da su rika kula kar wasu kungiyoyin damfara, wadanda ke karyar cewa su bangarori ne na hukumar ta NYSC su domin kawai su cuce su.
Hukumar ta NYSC ta yi nuni da sojan gona da wata kungiya mai amfani da dandalin www.nysconline.com.ng a matsayin wani sashi na hukumar ta NYSC, ta jaddada cewa duk wani dalibi ko matashin da ya yi wata harka da dandalin www.nysconline.com.ng din to ya kuka da kansa.
Daga karshe hukumar ta NYSC tayi Allah wadai da irin wannan tabi'ar da kuma gargadi ga matasa da su guji amfani da irin wannan dandali, masu anfani da shi kuma zasu kuka da kansu idan suka shiga hannun hukuma.