Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zauren Matasa – Kan Matsalar Rashin Tarbiyantar Da Yara


Yara 'Yan gudun hijira a makarantar firamare a Damare, Yola2
Yara 'Yan gudun hijira a makarantar firamare a Damare, Yola2

Cikin shirin mu na zauren matasa wanda Sunusi Adamu ya jagoranta, sun tattauna ne akan matsalar hayayyafar ‘ya ‘yan da ba’a iya baiwa tarbiyar da ta dace.

Tambayar farko cikin wannan zama dai itace, shin wake da hakki na tarbiyyar da yara? Malam Mohammed Haruna, yace uba ne keda hakkin tarbiyartar da yara, saboda duk abinda da ya faru a gida yana kan maigida abinda ya hada da mahaifiyar yaran da kuma ‘dau kacin yaran dake gidan, duk a karkashinsa suke. Hakin uba ne ya lura da duk abubuwan da yaran sa keyi, missali idan aka tura su makaranta a tabbatar da sunje kasancewar wani lokaci zasu iya tafiya dandamali suyi wasa alokacin da aka aika su karatu. Illimi dai shine ginshikin rayuwa idan yara basu taso da ilimi ba to zasu iya fadawa cikin kowanne irin hali.

Shikuma mallam Ibrahim Bamaiyi, na ganin abinda ya shafi lamarin tarbiya da kula da yara na uba ne da uwa baki daya, haka idan har uba baiyi wa yara tattali mai kyau ba to daga nan matsala zata fara faruwa, kasancewar yara na iya fara ziyartar gidan makwabta domin kwadayi kafin ma yakai ga zuwa makaranta. Yana da matukar amfani ga iyaye su tabbatar da cewa, sun mai da hankali wajen kula da ‘ya ‘yan su ta hanyar ciyarwa, tufatar wa, da huduba mai kyau. Da zarar sun fara zuwa makaranta to ya zama wajibi a dinga lura da aiyukan da suke a makaranta.

Hakkin makwabci akan wannan kuwa shine zamantakewa na fadawa juna gaskiya, idan kuwa makwabci yaga yara nayin wani abu da bai kamata ba, yayi magana har sau uku amma yaga cewa ba’a dauka ba, tabbas zai maida hankali kan renon nasa ‘ya ‘yan ne.

XS
SM
MD
LG