Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lauyoyi Matasa Sun Shigo Zauren Tattaunawar Mu


Daga Hagu zuwa Dama: Comrade Danjuma Bello Sarki, Shugaban Matasa na yakin neman zaben gwamna Yero da Bajoga a karkashin tutar jam’iyar PDP a Giwa, jahar Kaduna, da Shugaban Matasan jam’iyar PDP na Kaduna ta tsakiya: da Shugaban Matasan jam’iyar PDP na ja
Daga Hagu zuwa Dama: Comrade Danjuma Bello Sarki, Shugaban Matasa na yakin neman zaben gwamna Yero da Bajoga a karkashin tutar jam’iyar PDP a Giwa, jahar Kaduna, da Shugaban Matasan jam’iyar PDP na Kaduna ta tsakiya: da Shugaban Matasan jam’iyar PDP na ja

A cikin zauren tattaunawar mu na yau wakilin mu Abdulwahab Muhammed, ya zauna da wasu lauyoyi kuma matasa daga arewanin Najeriya, domin magana akan matsalolin dake shafar matasa, da bukatun matasa ga shugabannin da aka zaba.

Daya daga cikin lauyoyin dai tayi magana akan yadda matasa ke fitowa da tayar da hankali alokacin zabe, amma da zarar zabe ya wuce sai shugabannin da aka zaba su manta da matasan, ba tare da sunyi wani abu da zai amfani matasa. Hakan shike janyo rashin zaman lafiya da kiyayya tsakanin mutane musammam ma matasa.

Anyi kira ga mutane da su san ‘yancinsu, kasancewar duk mutanen da aka zaba domin shugabantar mutane idan har basuyi aikin da yakamata ba, mutanen da suka zabi wannan shugaba zasu iya yin amfani da dokar tsarin mulki domin sauke shugaban, kasancewar mutane basu san irin kudaden da ake ba ‘yan majalisu dake wakiltar yankuna, domin suyi wa mazabarsu aiki.

Idan aka samu rashin wakilci na gari ga wanda aka zaba domin wakiltar wani yanki, su mutanen wannan mazaba zasu iya bude wata takarda da neman sa hannun mutanen dake mazabar ko yankin, adadin mutanen da aka samu suka rattaba hannu kan takardar, zasu iya daukar takardar zuwa majalisa su kuma yi bayanin cewa yawan mutanen da suka saka hannu cikin takardar sun amince da cewa wikilin da suka zaba bai yi musu wakilci na gari ba, a saboda haka suna son a dawo dashi, dokar kasa ta tabbatar da wannan damar ba ta kundin tsarin mulki.

Daga karshe lauyoyin sunyi kira ga matasa da su san ‘yancin kansu, domin hakan shine zai kawo cigaban kasa da tabbatar da cewa duk mutanen da aka zaba su wakilci mutane suna yin aikin daya kamata ga al’umma.

XS
SM
MD
LG