A wannan zamani ana iya hada aikin jarida da sana’a domin samin kudin shiga harma da samar da aikin yi. Mallam Kabiru Danladi Lawanti na sashen koyar da aikin jarida a jami’ar Ahmadu Bello zariya, yayi karin haske akan tabbatar da hakan.
Hada aikin jarida da sana’a ana kiran sa Entrepreneurial Journalism a turance, kuma ba wani dadewa yayi da fitowa ba, an dai fara tunanin fito da hakan ne alokacin da yanar gizo ta fara warwasuwa a shekara ta alif dari tara da casa’in, an dai kirkirota a dalilin yadda za’a iya samar wa da gidajen jaridu kudi.
Bude wani dandali akan yanar gizo da zai zamanto na nishadantarwa ko ilimantarwa, da samun mutane masu dinbin yawa su rika ziyartar wannan dandali, da zarar mutanen dake ziyarta sun kai adadin da ake bukata, sauran kamfanoni na iya neman mai shafin domin bashi damar kasuwanci da wannna shafin dandalin ta wajen yin tallace tallace, kuma mutum nada wani kaso cikin tallace tallace da kamfanin keyi. Babban abin shine yin amfani da shafin yanar gizo wajen yada manufofi ta yadda za’a iya jawo hankulan jama’a da canza yadda tunanin mutane yake ta yadda ake aiwatar da wasu abubuwa.