Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Chelsea Ta Kammala Sayen Dan Wasan Barcelona Pedro


Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta kammala sayen dan wasan FC Barcelona, Pedro a kan tsabar kudi Euro miliyan 30, kuma har ya rattaba hannun buga ma zakarun na firimiya lig tamaula.

A yau alhamis FC Barcelona ta dauke ma Pedro nauyin zuwa wurin furatis, inda ya haye jirgin sama zuwa London, likitoci suka duba shi suka tabbatar da lafiyarsa.

Duk wannan abu ya faru ne a bayan da ita kungiyar ta Chelsea ta sace ma kungiyar Manchester United wannan dan wasan da su ‘yan Man U suka jima suna zawarci.

Pedro ya fadawa shafin Chelsea na intanet cewa, “Nayi farin cikin zuwa nan, ina murna zan fara buga ma Chelsea tamaula, kuma nazo nan ne domin ci gaba da lashe kofuna.” Pedro yace ya godewa kulob din da magoya bayanta saboda ba shi damar sanya rigar wasa ta kulob din mai lakabin Blues.

FC Barcelona ma ta fitar da sanarwa tana fadin cewa ita da Chelsea sun cimma daidaituwa a kan sayarwa da sayen Pedro a kan Euro miliyan 30. “FC Barcelona tana bayyana godiyarta ga Pedro Rodriguez a saboda halin kwarewa da kuma sadaukar da kai a lokacin da yake kulob din, tare da yi masa fatar alheri a nan gaba.” In ji wannan sanarwa ta FC Barcelona.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG