Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fuskoki Biyu Na Pep Guardiola


Coach Pep Guardiola
Coach Pep Guardiola

Jamus na kan gaba wajen yawan jefa kwallaye a ragar wasu kungiyoyin kwallon kafa fiye da kowa a gasar cin kofin rukunin kwararru na ‘Champions League’. Sai dai a lokacin da mai horar da ‘yan wasan su ke tare da kungiyar wasan kwallon kafa ta Barcelona, kwarara kwallo daga kusurwa da sa mata kai ta shiga raga ba shi cikin jinin kungiyar.

A boye ko a bayyane, wannan shine kololuwar bambancin daukaka tsakanin yadda kulub din Barcelona na Pep Guardiola ke buga wasa da kuma yadda kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ke taka wasa a lokacin da yake jagorantarsu.

Daga cikin kwallaye fiye da 100 kulob din Barcelona ya jefa a ragar abokan karawa, kwallo guda 1 kacal ake samu daga cikin kwallaye 16 wadan da aka jefa a raga ta hanyar anfani da kai.

Lokacin da yake kulob din Bayern, kididdigar ta yi kusa ne da kwallo guda 1 daga cikin guda 5 da ake jefawa a raga ta hanyar anfani da kai. Wannan shine ya bambanta yanayin jagorancinsa a Bayern da Barcelona, wato fuska biyun koyarwar sa kenan.

Wani tsohon dan wasan Bayern kuma tsohon zakara a kungiyar kwallo ta Liverpool Dietmar Hamann yace, da wuya kaga Barcelona tana kwararo kwallo ta kusurwa ko kaga suna wasan sama, sai dai kawai ka ga suna taka wasa da karfinsu.

XS
SM
MD
LG