Alexis Sanchez, ya zama dan kwallon na farko da ya jefa kwallaye fiye da ashirin, a kakar kwallonsa na farko, a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, tun bayan Thierry Henry, inji Arsene Wenger, ya kuma ce dan kwallon yayi abun bajinta.
Dan shekaru ashirin da shida, Sanchez, ya jefawa Arsenal, kwallaye, biyu, a raga a wasan su da Hull City, a jiya, an dai tashi wasan uku da daya, wanda ya kawo yawan kwallayen da Sanchez, ya jefa a raga a kakar bana zuwa ashirin da hudu.
Dan wasan na tsakiya ya kuma taimaka wajen jefa wasu kwallaye goma sha daya, cikin kuzarin da ya kara karfafa ma kungiyar Arsenal har ta samu maki ashirin da takwas cikin talatin, na neman shiga gasar cin kofin zakarun kulob kulob na Turai a shekara ta goma sha takwas, a jere.
A farkon kakar kwallon bana shahararran dan wasan nan wato Henry, wanda ya ciwa Arsenal, jimilar kwallaye dari da saba’in da biyar, a gasar frimiya lig, yace daukar Sanchez, da Wenger, yayi ya kasance babban kamu da yayi a shekaru shida, da suka wuce.