Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hattara Dai Matasa Masu Rubuce Rubuce A Yanar Gizo


Ethiopia-Tablets as Teachers
Ethiopia-Tablets as Teachers

Rundunar 'yan sanda a jahar Legas ta gurfanar dawani matashi mai mu'amula da shafin Bloga mai suna Desmond Chima a gaban kuliya bisa zargin sa da ake yi da aikata batanci ga shugaban bankin UBA na Najeriya Mr Philiph Odohza.

Jami'an 'yan sandan sun cafke matashinne a sakamakon zarginsa da suka yi da yin rubuce rubucen batanci a agame da mutumin tare da zargin cewa yana hulda da wata farkar sa.

A ta bakin lauya mai shigar da kara, Henry Obiazie, wanda ake zargin ya saba ma dokar kundin tsarin mulkin kasa da ya shafi hada hada da mu'a mulla ta kafofin sadarwar zamani, sashi na 24 da lamba daya cikin baka na kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 2015.

Wanda ake karar tare da wasu wadanda aka ce yanzu haka ana neman su ruwa a jallo, sun aikata wannan lafi ne a jahar Legas.

Wanda ake karar dai ya musunta zargin da ake masa, a yayin da babban alkali Muhammed Yunusa na babbar kotun tararyya da ke birnin Legas ya dage shari'ar har wani lokaci da ba'a fada ba. Wannan ba shine karo na farko ba da ake zargin ana anfani da kafar sadarwar facebook da sauran su domin cin zarafin manyan mutane.

Saurari cikakken rahoton Babangida Jiril daga Legas.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG