Haduwar da Kasar Mexico da Najeriya bayan buge kasar Ecuador da ci biyu (2) da nema (0) a zagayen kusa da na karshe a gasar kwallon kafar FIFA na ‘yan kasa da shekaru 17 ya ja zakuwar shirin kallon wasan. Harin Claudio Zamudio a kashin lokaci na farko da kuma bugun daga kai sai mai tsaron gidan da Bryan Salazar yayi bayan dawowa daga hutun lokaci shine ya yi wancakali da kasar Yammacin Amurkar.
Wanda suka gaza cimma kwazonsu da ya gabata a wasan da suka buga a zagayen kusa da na karshe a shekarar alif dari tara da casa'in da biyar. Dama kasar ta Ecuador ta kara tsayin daraja ne sakamakon zazzafan kwasar bugun kwallon John Pereira don karya lagon masu tsaron gidan Mexico, inda kwallon ta bugi turken ragarsu ta fada.
Abin tunawa a wannan wasan shine yadda Mexico ta yi ta dakon wannan kwallo a raga, sai dai ba kasafai takan karaya da farmakin na kasar Ecaudor a ragarta ba, wannan wasa ne da ake jiran gani na zakarun lashe gasar har sau hudum a baya.