Biyo bayan sallamar da aka yi wa wadansu jami’an kwastam 5 masu mukamin mataimakin mukaddashi, da kuma wasu 34 a satin da ya gabata, akwai yiwuwar wasu sauran ma'aikatan hukumar har 400 zasu bar aiki da hukumar a sakamakon wasu dalilan da suka hada da cin hanci da rashawa, da rashin bin ka’idojin aiki, da rashin biyayya, da kuma rashin kasancewa a wuraren ayyukan su.
Kuma rahotanni sun nuna cewar a cikin wadanda za’a sallama daga aikin da dama ana zargin su da lafin canza wa kansu wuraren ayyuka da kuma bin wasu hanyoyi domin kara ma kamsu girma koda lokacin kara masu girmn bai yi ba.
Mujallar Vangurd ta bada rahoton cewa yawancin wadanda suka ki bin umurnin canza masu wurin aikin, sun yi anfani ne da takardun neman alfarma da suka amso daga warin wasu ‘yan majalisu wadanda suka nemar masu alfarma daga babban ofishin hukumar.