Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Aka Kaddamar Da Manhajar Toshe Kafar Satar Bayanan Wayar Hannu


A yau talata kamfanin Google zai fito da wasu muhimman manhajoji guda 23 domin yin gyara ga babbar manhajarsa ta Android mai tafiyar da wayoyin hannu.

Biyu daga cikin wadannan gyare-gyare an bayyana su da cewa masu matukar muhimmanci ne. Daya daga cikinsu zai nemi toshe kafar da wani daga nesa zai iya satar bayanan dake cikin wayar hannu ta mutum ta hanyar sanya masa wata boyayyiyar manhaja ta email, ko a lokacin da yake browsing ko ta hanyar sakon text message mai hoto, MMS.

Kamfanonin tsaron wayoyi da kwamfuta irinsu Trend Micro, System Security Lab da Keen Team, har ma da sashen tsaron wayoyin hannu masu aiki da manhajar Android na kamfanin Google, sune suka gano wadannan matsalolin.

Babbar ayar tambaya ga masu amfani da wayoyin hannu na Android a yanzu ita ce yaushe ne wadannan muhimman manhajoji na toshe kofar satar bayanansu zasu isa ga wayoyinsu. Kamfanin Google zai tura wadannan manhajojin yin gyara kai tsaye ga duk masu yin amfani da na’urorin Nexus, yayin da kamfanin Samsung yace zai tura su kai tsaye ga masu amfani da wayoyinsa samfurorin Galaxy S Note da kuma Tab.

Kamfanin LG ma yace a duk wata yana tura wadannan ga masu amfani da wayoyinsa, Sauran kamfanonin kera wayoyin hannu irinsu HTC da Sony sun tura manhajar gyara kamar ta Stagefright ga masu amfani da wayoyinsu amma kuma basu ce zasu rika tura irin wadannan manhajojin gyara kai tsaye a duk lokacin da suka fito ba.

Idan mai sauraro yana da wayar Android mai amfani da Marshmallow ko fitowa ta 6 ta Android, zai iya duba wayarsa ya ga ko an tura masa da wannan manhaja ta gyaran tsaro. Za a iya zuwa Settings, a duba inda aka rubuta Android Security Patch. Idan mutum ya ga an sanya ranar da aka turo na baya-bayan nan ta yi dai da 1 ga watan Nuwamba, to yana da sabuwar manhajar ta toshe kafar satar bayanan wayarsa daga nesa.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG