Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar NDLEA Ta Cafke Mutane 22


Hukumar kula da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jahar Gombe ta cafke wasu mutane 22 wadanda take zargi da fataucin miyagun kwayoyi harma ta kwace kwayoyin da nauyin su ya kaikilogiram 77.99

A cewar kwamandan hukumar jahar Mr Adole, ya bayyana wa hukumar yada labaran jahar cewa hukumar ta kara fadada ayyukan ta zuwa yankunan karkara a Dadin kowa na garin Yamaltu/Deba, da yankinj karamar hukumar dukku.

A tsakanin watan Yuli da Oktoba, hukumar ta kama kilogiram 77.99 na miyagun kwayoyi a jahar ta Gombe. Kuma yanzu haka akwai mutane 22 da ke hannun hukumar.

Dalilin haka yasa ma'aikatan hukumar ke ziyartar wurare daban daban a fadin jahar jahar. ya kara da cewa wanna ya taimaka ma hukumar gudanar da ayyukan ta ba kakkautawa.

Mr Adole ya nuna godiya da jin dadi musamman ga kotun da yace take aiki tare da su hukumar.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG