Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Italiya Ta Ceto Bakin Haure Fiye Da Dubu 4 Cikin Kwanaki Biyu Rak A Tekun Bahar Rum - 9/4/2014


Wani jirgin ruwan yakin Italiya ya doshi wani jirgin ruwa dauke da bakin haure a tekun Bahar Rum, kusa da tsibirin Lampedusa
Wani jirgin ruwan yakin Italiya ya doshi wani jirgin ruwa dauke da bakin haure a tekun Bahar Rum, kusa da tsibirin Lampedusa
Italiya ta ce a cikin kwanaki biyun da suka shige, ta ceto bakin haure su dubu 4 daga cikin tekun bahar Rum.

Ministan harkokin cikin gidan Italiya, Angelino Alfano, ya fadawa gidan rediyon kasar yau laraba cewa bakin haure su na isa kasar babu kakkautawa, haka ma aikin ceto wadanda suka makale cikin teku, yana mai fadin cewa wannan matsala tana kara yin muni sosai.
Ya bukaci KTT da ta kara mikewa domin sintiri a tekun Bahar Rum, yana mai fadin cewa miliyoyin dalolin da aka kashe sun kasa warware wannan matsalar.

Italiya ta zamo tamkar kofar shiga Turai ga ‘yan Afirka dake kokarin tserewa daga talauci da yaki da yamutsin siyasa.

Italiya ta kaddamar da shirin dindindin na ceto mutane daga ruwan teku a bayan da wasu bakin haure su fiye da 400 suka mutu a karshen shekarar da ta shige a wasu jiragen ruwa biyu da suka yi hatsari dab da gabar kasar.
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:39 0:00
Direct link
XS
SM
MD
LG