WASHINGTON, DC —
Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya fadawa ‘yan majalisar dattijan Amurka cewa kasar Rasha ce take rura wutar aware a yankin gabashin Ukraine, domin abinda ya kira kitsa tashin hankalin da zai ba ta hujjar kai farmakin soja.
Kerry ya fadawa kwamitin hulda da kasashen waje na majalisar dattijai cewa a fili yake irin hannun da Rasha ke da shi a tashe tashen hankulan nuna goyon bayan Rasha a birane akalla 3 na Ukraine. Yace shugaba Obama yana tsara matakan takunkumi masu tsauri da zai dauka idan Rasha ta ci gaba da kokarin gurgunta Ukraine.
Tun da fari a yau talata, ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov ya fadawa ‘yan jarida a Moscow cewa ya kamata a sanya yankunan kudu maso gabashin Ukraine a cikin duk wata tattaunawar da za a yi kan makomar kasar. Yace Rasha tana son ganin an wakilci wadannan yankunan da akasarin jama’arsu masu magana da harshen Rasha ne a duk wata tattaunawa ta bangarorin.