Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ban Ki Moon Yace Afirka Ta Tsakiya Tana Kan Siradi - 6/4/2014


Babban sakataren MDD, Ban Ki-moon yana Kigali yau lahadi domin kewayowar shekaru 20 da kisan kare dangin da aka yi a Rwanda. Kafin ya isa nan, ya yada zango a Jamhuriuyar Afirka ta Tsakiya, inda ya shaidawa majalisar dokokin wucin gadi cewa kasar ta shiga cikin yamutsi.

Mr. Ban yace shekaru 20 da suka shige, kasashen duniya sun ci amanar mutanen Rwanda, kuma a yanzu, su na nuna gazawa wajen tallafawa al’ummar Afirka ta Tsakiya. Yace ana aikata munanan ayyukan ta’asa na kare dangi kan wasu jinsuna da addini a kasar.

Ban ya ziyarci wani sansani inda mutane dubu 60 suke zaune a wajen babban filin jirgin saman Bangui, sannan ya ziyarci babban masallacin birnin, inda fararen hula kimanin dubu 10 suka buya. Akwai ‘yan banga mabiya addinin kirista da ake kira Anti-Balaka dake musu barazana a waje, duk da cewa an girka sojoji a kewayen masallacin.

A masallacin mutane sun rike kwalaye suna neman da a kwashe su zuwa wasu wurare, wasu kuma na neman da a raba kasar kawai, yayin da dubun dubatan Musulmi ke ta gudu zuwa yankin arewa maso gabas wanda har yanzu yana hannun tsoffin ‘yabn tawayen Seleka wadanda akasarinsu Musulmi ne
XS
SM
MD
LG