Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamafanin Twitter na Shirin Yin Wasu Sauye-Sauye


Kamfanin sada zumuncin twitter ya ce ya na duba karin chanje-chanjen da za su saukaka yin amfani da shafin, bayan wani rahoto kwanan nan game da ayyukan kamfanin, wanda ya nuna cewa babu wata riba da aka samu, sai ma hasarar dala miliyan 90 da kamfanin ya tafka.
Duk da cewa kamfani fitaccen ne ga masu amfani da hanyoyin sada zumuncin zamani, twitter ya fuskanci gasa daga takwarorinsa kamar su Facebook da Snapchat da kuma Instagram.
Shafin twitter ya fuskanci korafe-korafe game da wahalar yin amfani da shi in aka danganta shi da sauran shafuka, da kuma yadda akan dole masu amfani da shafin ke rubutun da baya wuce kalmomi 140 kuma sai sun yi amfani da wasu harrufa na musamman don yin wasu abubuwan, missali kamar sake tura rubutun wani.
Shugaban kamfanin Jack Dorsey, ya fadi cewa biyo bayan rahoton na baya-bayan nan, wanda ya nuna alkaluman wadanda ke amfani da shafin a shekara ya ragu. Mutane miliyan 307 su ka yi amfani da shi a shekarar 2014 amma a ta 2015 sun ragu zuwa miliyan 305. Duk da dai hasarar dala miliyan 90.2 din da kamfanin ya yi a shekarar 2015, ba ta kai ta shekarar 2014 ba inda kamfanin ya tafka hasarar dala miliyan 125.
Dorsey ya ce, sauye-sauyen da kamfanin zai yi bana sun hada da saukaka hanyar yin amfani shafin da kuma yi wa tsarin daukar hoton bidiyo kai tsaye garanbawul. Ya kuma ambaci cewa ta yiwu a chanza tsarin yin amfani da kalmomi 140 kacal wajen yin rubutu.

XS
SM
MD
LG