A jamhuriyar nijer yau aka yi bukin kaddamar da soma aiyukan kafa wata masana’antar sarrafa albasa a ci gaba da yunkurin tallafawa manoma samun hanyoyin sayar da anfanin gona da daraja.
A kalla million dubu 12 na cfa ne za a kashe domin aiyukan gina wannan masana’anta mai mazauni a garin madawa na karkarar tawa. Ana hasashen cewa masana’antar mai suna SOTRACO SA za ta sayi tone dubu 22 na albasa a kowace shekara daga hannun mazauna karkara.
Kimanin tone dubu 5OO ne manoman albasa ke samarwa a kowace shekara sai dai su na fuskantar matsaloli kafin su shigarda wannan anfanin noma zuwa ketare saboda haka daraktan bunkasa aiyukan noma na kasar nijer ALHAJI ABDU UMANI ke ganin ta hanyar wannan sabuwar masana’antar sarrafa albasa matsalolin sun kusa zama tarihi .
Masu saka hannun jari daga kasashe kamar Burkina faso Ghana da Najeriya da suka halarci wannan buki sun bayyana kyaKkyawan fata a game da alfanun da aiyukan sarrafa albasar zai kawowa manoma da masu kasuwancin albasa .
A daya bangare, ta dalilin wannan masana’antar sarrafa albasa dimbin matasan kasashen yankin afrika ta yamma ne zasu sami aikin yi abinda zai kara taimakawa a yaki talauci da sauran miyagun aiyukan da zaman kashe wando ke jefa matasa a yau.