Kila a shawo kan matasan kungiyar Kato Da Gora shiga aikin soja, domin taimakawa wajen yaki da yan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Nigeria.
Dan takarar majalisar dokoki daga jihar Borno, Alhaji Abdulkadiri Rahis ne ya bayyana haka a wata hira da aka yi dashi.
Yace idan Buhari ya zama shugaban kasar Najeriya, to zai san darajar rayukan matasa da suka sadaukar da rayukansu domin kare kasarsu.
Yace, “duk ‘ya ‘yan kungiyoyin aikin sa kai na matasa, wadanda ake cewa Civilian JTF da turanci, na birnin Maiduguri da wasu bangarorin Jihar Borno, za’a shigar dasu aikin soja dama sauran ayyukan da suka shafi aikin tsaro, idan Janal Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasar Najeriya.”
Ya dai ce babu wata gwamnati kirki da zata guji amfani da matasan da suka sadaukar da ran su, harma suka bar iyalansu domin su kare birnin Maiduguri dama wasu sassan jihar Borno daga ta’addancin mahara, wanda ke kashe mutane da ruguza garuruwan su.
Ya kuma kara da cewa, babu wata gwamnati ko wani mutum da zai yi na’am ko amincewa da irin barna da mumunar da ake yiwa mutanen da basu jiba basu gani ba. Ya dai ce wannan na daya daga cikin dalilan da suka sa ya shiga siyasa, domin tabbatar da bege na, cewa dan talaka ma zai iya yin shugabanci ya jan ragamar mulki.
Yace Idan har aka zabe shi a matsayin wakilin majalisar wakilai, zai tabbatar dukkan matasa a mazabar sa, su samu aikin yi zamu tabbatar da samar musu hanyoyin kasuwanci.
Kungiyar ‘yan kato da gora ta matasa ce dake yakar maharani Boko Haram daga kwace yawancin yankunan jihar Borno.