Bayan kwashe watanni da aka yi ana jayayya tsakanin hukumar tsaro ta FBI da kamfanin Apple, yanzu haka FBI tace ta samo wata hanya da zata iya bude wayar iphone din nan mallakar dan bindigar da ya kashe mutane a garin San Bernardino.
Ma’aikatar Shari’a ta Amurka tace an nunawa FBI hanyar da zasu iya bude wayar, haka kuma lauyoyin ma’aikatar sun bukaci babban alkalin tarayya da ya soke zaman da za’ayi na yau Talata domin a sami lokacin da za a iya gwadan sabuwar hanyar.
Sama da watanni biyu kenan ake ta takaddama tsakanin Apple da FBI, wanda har ya janyo cece kuce a duniya baki daya, bayan da kamfanin Apple ya hau kujerar naki domin kare sirri da bayanan abokan cinikayyarsa. Duk da cewa a kwai manufofi da dama da suka haramta wa kamfani damar bada bayanan jama’ar da ke amfani da kayan sa.