A yau mun sami zantawa da malama Hassana wata matashiya mai sana'ar saye da sayarwa domin ta zama mai dogaro da kai, kuma ta ce tana da dilpomarta amma hakan bai hana mata sana'ar ta ba.
Kamar yadda matashiyar ta baiyana cewar dogaro dakai nada matukar amfani ga dukkan matasa, lallai wannan magana haka take domin kuwa hakan na kara ma iyali samun saukin rayuwa domin takan taimaka wajan rage nauyi da yawa a kan mai gida.
Hassana Ibrahim ta ce tana amfani da hanyoyin sadarwa na zamani domin tallata kayan ta, wato ba sai ta fita shago ko kuma tabi gida gida ba kafin ta sayar da kayan ta. Ta kara da cewa takan yi amfani da manhajar WhatsAp ko facebook domin nuna irin kayan da take dasu na sayar wa a lokaci kuma tana samun kasuwa kwarai.
Ga cikakkiyar hirar.