Jami’an tsaro sun cafke wani matashi mai shekaru 30 da haihuwa a sakamakon zargin sa da aka yi na yiwa wata yarinya mai shekaru bakwai da haihuwa fyade a layin da aka fi sani da Arab road dake Kubwa, a birnin Abuja.
Mutumin da ake zargin mai suna Joshua, yana da ‘ya’ya uku, kuma kamar yadda rahotanni suka bayyana, ya ja yarinyar zuwa cikin gidan sa ne a yayin da take hanaya zuwa gida inda ya aikata wannan danyen aiki da ita.
Rahotanni sun bayyana cewa mahaifiyra yariyar ta aike ta ne da debo ruwa a yayin da matashin ya ja yariyar mai suna Hafsat zuwa cikin gidan sa, kuma ya garkame daki da ita, da yin amfani da karfi wajan toshe mata baki sa’annan yayi lalata da ita.
Majiyar ta bayyana cewa fitowar yarinyar keda wuya sai ta garzaya gida inda ta fadawa innar ta abinda ya faru da ita, wanda hakan yasa uwar Hafsat ta sanar da ‘yansanda ba tare da bata lokaci ba.