A yau dai daga ganin ‘Dan Iya, nace ‘dan uwa zo muyi maganar zabe, don kasan nifa inda za’a bani kudi kawai nake nema in lababe, duk ‘dan siyasar daya mika min kudi zan karbe, shiyasa duk inda ka ganni ina ‘dauke da katin zabe na, da an danka min kudin katin zaben zan dafasu in sabe.
Daga nan idan yaso in dan tani komai ya cabe, tunda dama komai a kasar ya kwararrabe, kayan more rayuwar da shuwagabannin mu na baya suka bari a kasar duk ya rube, da zarar manyan mu na yanzu sun ga dukiyar kasa sai su wawura kawai su gudu can waje su labe. Kuma a haka suke san zama kan mulki daram dam wai kada ya sullube.
Daga jin haka nace eh ‘Dan Iya duk da yake dai ta wani hannun ka fadi gaskiya, cewa shuwagabannin mu sun yiwa kasarmu tsiya tsiya, sun barmu muna ta famar shan wuya amma yana da kyau kasan idan kana san tsallakewa daga duk wata sakiya, ka kuma warware dukkanin sakakkiyar sarkakiya to fa wajibine ka zama mai juriya, ka guji halin hayaniya da haya gaga irin na kuruciya, da sannu dai wataran zaka ganka kana fariya, saboda abubuwa sun sauya ‘yan kasa kuma sun sami dama kowa zai sakata ya wataya.
‘Dan Iya yace, amma Allah ya rufa asiri dana ganka, ai ni da tuni na riga na yanke shawarar dora ganye ne aka, idan na samu mai kudi koda dubu uku ne sai in mika mai katin zabe na babu ruwana da wata suka, kasan ni idan babu kudi bana iya wata harka amma tunda kayi min wannan bayani tona farka, yanzu kan bani ba wata fuffuka, zan jira ranar zabe in fita cikin bin doka in jera cikin jerin majirata jefa kuri’a koda ana marka marka, saboda na fahimci ta hakane kawai zamu samu magance duk wata ‘baraka, ita kuma kasarmu ta hakane kawai zata samu ‘daukaka.
Nace to dan Iya Allah yabamu mafuta ya kuma raba mu da duk wata hanyar ‘bata, yasa ‘yan kasa duka suce su da saida kuri’arsu haihata-haihata Allah barshi kasarmu ta samu ta inganta, harma ta samu sabon sararin sauyin baiwa sauran kasashe rata.
Saurari ‘Dan Iya.