Mataimakan Koch din kungiyar Super Eagles sun karyata zargin wasu rahotanni da aka fitar na cewa suna aiki da kungiyar batare da sa hannu kan yarjejeniya ba.
Jean Francoise Luscuito da Salisu Yusuf ne suka tabbatar da hakan a sakateriyar hukumar kwallon kafar Najeriya NFF a jiya Talata.
Inda suka tabbatar da cewa sun rattaba hannu kan takardun yarjejeniya da hukumar tun da dadewa. inda sukace basu san ta inda wannan labari ya fito ba, saboda basu taba yin magana da kowa ba kan hakan, ko kan cewa ba’a basu albashi ba.
Sun kuma tabbatar da cewa suna aiki sosai da koch din kungiyar Sunday Oliseh ba tare da wata matsala ba. abinda suka sa gaba yanzu shine yadda zasu ga sun gina kungiyar, da ganin sun cimma burin hukumar NFF wajen ganin taka rawar da kungiyar take kada ta gushe.
Kwacakwacan dai zasu yi wani taro da shugaban hukumar kwallon Najeriya, Amaju Pinnick, domin tattaunawa kan shirinsu na wasan neman shiga gasar nahiyar Afirka mai zuwa ta shekara ta 2016, da zasu kara da kasar Burkina Faso cikin watan Oktoba.